Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: kungiyar Hizbullah ta yi kira ga Hukumar Beirut da ta gaggauta kiran jakadan Amurka a fadar Baabda domin ka masa kunne.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba, kungiyar Hizbullah ta soki matsayin Amurka da wakilin Amurka Tom Barak ya dauka a taron 'yan jaridun Lebanon a fadar Baabda, inda ya kwatanta yanayinsu da "dabbobi." Tabbas ba mu yi mamakin wannan wawanci, girman kai da cin zarafi na Amurka ba, amma muna kira ga mahukuntan Labanon da su gaggauta kiran jakadan Amurka su tsawata masa.
Mu’amalar da Barak ke yi wa ‘yan jaridan Lebanon da kuma kalaman batanci a kansu a yayin wani taron manema labarai a fadar shugaban kasa ta Baabda ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta tare da janyo martanoni da dama.
A taron manema labarai bayan ganawar da Barak ya yi da shugaban kasar Labanon, Joseph Aoun, a lokacin da ‘yan jaridun suka yi gaggawar yin tambayoyinsu, Barak ya yi musu jawabi da kalaman batanci, ya ce, “Ku nutsu ku kwantar da hankalinku, ina so in gaya muku wani abu, idan har kuka yi hargitsi, kuka zama kamar dabbobi, to zan bar nan.
Kafin ya amsa tambayoyi game da kwance damarar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Barak ya kuma ce, "Kuna son sanin abin da ke faruwa, to ku kasance masu yin halayyar irin ta masu wayewa".
Ofishin shugaban kasar Labanon ya kuma bayyana nadama kan kalaman da daya daga cikin bakinsa yayi tare da godewa dukkan 'yan jarida da wakilan kafafen yada labarai da ake girmamawa.
Barak ya jaddada a wani taron manema labarai da ya yi a kasar Lebanon a ranar Talata cewa, ‘yan mamaya na sahyoniyawan ba za su taba ja da baya ba, kafin a aiwatar da shirin musamman na gwamnatin Lebanon na takaita makamai a hannun gwamnati ba, kuma Tel Aviv za ta mayar da martani kan shirin na Beirut ta hanyar gabatar da nata shirin janyewa daga Lebanon.
Ya ce: Isra'ila ba za ta taba ficewa daga kasar Lebanon ba kafin a aiwatar da shirin gwamnatin Lebanon (na kwance damarar Hizbullah).
Barak ya ci gaba da da'awar cewa: Ba mu neman yakin basasa a Labanon kuma za mu yi kokarin tabbatar da ficewar Isra'ila daga kudancin Lebanon, amma mafi mahimmanci shi ne kwance damara na Hizbullah.
Wakilin na Amurka ya kara da cewa: Isra'ila za ta dauki matakai kwatankwacin matakin kwance damara na kungiyar Hizbullah, sannan gwamnatin Lebanon za ta gabatar da wani shiri na kwance damarar Hizbullah, kuma ina ganin wannan shiri zai yi nasara, kuma gwamnatin Lebanon ta gindaya sharudda 11 tare da daukar alkawarin yin aiki da su, wanda na farko shi ne kwance damarar Hizbullah.
A ranar Lahadin da ta gabata a wata ziyarar da ya kai yankunan da aka mamaye, ya gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
A cikin wannan ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan dakatar da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan kasar Labanon da kuma makomar alaka da kasar Siriya.
Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta sanar da cewa, Barak ya tattauna bukatar shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da hare-haren da gwamnatin kasar ke kaiwa Lebanon, da kuma batun tattaunawa da kasar Siriya a ganawarsa da Netanyahu.
Your Comment